NBS- Jihar Kano ta rabauta da sama da biliyan biyun don inganta muhalli

Jihar Kano ta karbi kaso mai tsoka daga kwamitin rabon arzikin kasa, wanda hakan ya sanya jihar zama kan gaba cikin jihohin kasar 36, a tsakanin watan yunin shekarar 2023, zuwa watan yunin wannan shekara.

Hukumar kididdiga ta kasa NBS ce ta fitar da rahoton dake nuna cewa jihar Kano a tsakanin lokacin ta rabauta da kudi naira Biliyan 2 da milyan daya, domin amfani da kudin wajen magance matsalolin da suka shafi muhalli a jihar.

Daga cikin manufar bayar da kudin gwamnatin tarayya na fatan jihohin kasar suyi amfani da kudin, wajen magance matsalolin muhalli irin su kwararowar hamada, ambaliyar ruwa, da kuma zaizayar kasa.

A yan shekarun da suka gabata, gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi naira Biliyan 38.62, wanda kuma jihar Kano ta zama kan gaba wajen karba naira miliyan 175 duk wata domin gudanar da wadancan ayyuka.

Rahoton yace Jihar Borno dake fama da matsalar masu tayar da kaya baya na boko haram da yadda muhalli ya salwanta a wannan jiha, bata kai Kano karbar kaso mai tsoka ba, domin kuwa Borno duk wat ana rabauta da naira Milyan 140 ne kaca, wato Kano ta bata tazarar naira miliyan 35 ke nan a yadda rahoton hukumar NBS ya bayyana.

Sassa da dama yanzu haka na jihar nan na fama da matsalar zaizayar kasa, musamman garin daba dake yankin karamar hukumar Dawakin Kudu, zaizayar kasar dake ci gabar da haifar da koma baya ga manoman yankin kuma a kullum kira suke ga gwamnati amma a cewarsu har yanzu shiru.

Shi dai wannan kudi akan ware kaso 2 cikin dari na arzikin kasa, tare da baiwa ofishin kula da asusun taimakawa muhallin wanda ke karkashin ofishin sakataren gwamnatin tarayya, kuma tun a shekarar 1981 aka fara wannan tsari.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 15 hours 27 minutes 55 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 9 minutes 20 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com