Home Labarai Sojojin Nijeriya sun hallaka kwamandan Boko haram, Abu Rijab, a jihar Borno

Sojojin Nijeriya sun hallaka kwamandan Boko haram, Abu Rijab, a jihar Borno

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarun ta sun sami nasarar hallaka kwamandan mayakan kungiyar Boko haram Abu Rijab da wasu mayakan kungiyar sakamakon wani hari da dakarun sojin suka kai a ranar asabar.

Wannan dai na cikin wata sanarwar da mai Magana da yawun ya wallafa a shafin hukumar na X, wanda yace dakarun sun sami nasarar ne sakamakon wani sumame da suka kai garin Bula Daloye dake karamar hukumar Bama a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Yace wannan nasarar ta samu ne sakamakon mika wuya da mayakan ke cigaba da yi su da iyalan su ga dakarun sojoji, bayan matsa kaimi da dakarun ke yi a maboyar ‘yan ta’addan.

Haka kuma sojojin sun sami nasarar kama wadanda ake zargi da aikata ta’addanci tare kuma da kwato bindigu da alburusai.

“bayan musayar wuta da dakarun mu sukayi da ‘yan ta’adda sun sami nasarar hallaka kwamandan kungiyra boko haram Abu Rijab da kuma mayakan kungiyar guda uku.

“kuma sumamen ya kai ga kwato bindiga kirar AK-47 da kuma wayoyin hannu.

“haka kuma Karin ‘yan ta’adda takwas da iyalansu sun mika wuya a karamar hukumar Gwoza.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp