Sojojin Nijeriya zasu gudanar da bincike kan abin ya faru a Kaduna

Babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin da ya faru a kasuwar Sabon Birni da ke jihar KAduna domin gano haƙianin abinda ya faru, da kuma kamo wadanda ake zargi.

Cikin wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta, an ga yadda wasu da aka yi zargin sojoji ne sun kashe mutum uku tare da shanu a ƙalla 100 a kasuwar Sabon Birni da ke yankin ƙaramar hukumar Igabi a jhar Kaduna.

To sai dai cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya ta fitar ta hannun daraktan yaɗa labaranta, Onyema Nwachukwu, ta jajanta wa iyalan al’ummar yankin Sabon Birni da mutanen da lamarin ya shafa, tare da alƙawarta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

”Kuma duk jami’in da muka samu da hannu a wannan lamarin, to za mu ɗauki matakin da ya dace a kansa”, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

Sanarwar ta ci gaba da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ɗora wa rundunar sojin ƙasa ta Najeriya alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, don haka ba za ta lamunci duk wani yunƙurin saɓanin hakan ba.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1240 days 7 hours 28 minutes 28 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1222 days 9 hours 9 minutes 53 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com