Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce yayi matukar kaduwa da jin yadda yan bindiga suka kashe sarkin Gobir,tare da cin alwashin daukar mataki akan masu garkuwa.
A cikin sanarwar da mai Magana da yawun shugaban Najeriya Ajuri Ngelele ya fitar, ya ce shugaban ya bayyana kisan basaraken a matsayin cin zarafi da kuma tozarci da bazai bari a cigaba da aikawa ba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya kumayi ta’aziyya ga iyalan marigayin, da masarautar Gobir da ma gwamnatin Sokoto.
Ya kuma yiwa ‘yan Najeriya albishir da cewar gwamnatinsa a shirye take wajan yakin ayyukan ‘yan ta’addah.
shugaban ya bayyana cewar yana yin duk mai yuwuwa wajan ganin ya tabbatar da tsaro a kasar, sai ‘yan siyasa da al’ummar kasar na cigaba da bayyana takaicin su gane da rashin tsaro da yafi kamari a yankin arewacin kasar.












