Karo na 10 kenan da ake gudanar da bikin ranar hausa ta duniya dukkan shekara, an shirya bikin ne domin kara fadada harshen a duniya da kuma kara samun kyakkyawar alaka tsakanin Hausawa da abokan zaman su.
A hannu guda akan yi amfani da ranar wajen kara tunatar da juna hanyoyin da ya kamata abi domin fidda A’I daga rogo, daga matsalolin dake addabar su kama daga tsaro, hadin kai da dai sauransu.
Albarkacin wannan rana PRNigeria ta tattaunawa da wanda ya fara kawo shawarar gudanar da bikin ranar hausa. Abdulbaki Jari, Dan Jarida ne dake Aiki da kafar yada labarai ta TRT Africa dake Turkiyya.
Inda yace an fara samar da wannan rana ne a shafin Twitter wanda yanzu ya koma X, da zummar dawo da hankalin al’umma wajen nemo bakin zaren matsalolin dake addabar su.
Read Also:
“Ranar hausa ta samo asali a shafin twitter wanda yanzu ya koma shafin X, mun fara wannan biki ne a ranar 26 ga watan Agustan 2015, a lokacin nazo da shawarar cewa ya kamata yadda muke da yawa mu ware wata rana da zamu rinka tattaunawa da harshen hausa domin tunatar da juna tasirin harshe da kuma al’ada da kuma abu mafi muhimmaci wanda shine hadin kai.
Yace sun dauki wannan mataki ne kan yadda suka ga ana zuwa shafin sada zumunta ana fada ana tattauna wasu batutuwa da basu da muhimmanci, mai ma kon tattauna masu muhimmanci.
“Maimakon ya zama ana amfani da shafukan ana wayar da kai da zummar ganin cewa an nema maganin wadannan matsalolin musamman ta hanyar ankarar da shuwagabanni”
“Allah cikin ikon shi da aka yi wannan kira mutane sun amsa kiran inda wasu suka zo da shawarwari, wasu kuma suka zo da raha da sauransu ana kawo Karin Magana, wanda suma dai akwai hikima cikin Karin maganar, don kamar yadda muka sani ko wacce Karin Magana akwai hikima a ciki.
Taken bikin ranar hausan na bana dai shine, “tsintsiya madaurinki daya” hada kai domin inganta tattalin arziki da samar da zaman lafiya da tsaro.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 18 hours 16 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 58 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com