Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga manufar ma’aikatar ilimi ta tarayya na kayyade shekarun shiga jami’o’i, inda ya bayyana hakan a matsayin wani baƙon abu da zai janyo komabaya ga harkar ilimi a Najeriya
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana manufar a matsayin “zai haifar da naƙasu ga hakar ilimi” inda ya ce hakan ya saɓa wa ƙa’idojin tsarin ƙasar ta hanyar shiga ayyukan gwamnatocin jihohi.
Atiku ya yi nuni da cewa ilimi na cikin abubuwan da ke cikin ƙundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bai wa ƙananan hukumomin ƙasar karfi wajen tafiyar da harkokinsa.
Ya yi allah-wadai da matakin da gwamnati ta ɗauka na kafa manufofin ilimi ba kamar yadda doka ta tanada ba inda ya bayyana cewa hakan ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasa da kuma ɓata tsarin gwamnati.
Atiku ya ce, ‘Wannan sabon tsari na gwamnati ba zai yi tanadi ga dalibai masu hazaƙa ba wanda hakan ke nuna rashin mutunta hazaƙar ilimi.”
“Ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen zaƙulo ɗalibai masu hazaƙa tare da tallafa musu, ba tare da la’akari da shekarunsu ba” Atiku ya kara da cewa.
Atiku ya buƙaci da a bar wa gwamnatocin jahohi kula da harkokin ilimi, wanda a tunaninsa zai fi dacewa da yadda ake yi a ƙasashen duniya.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 4 hours 46 minutes 2 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 6 hours 27 minutes 27 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com