A yau ne Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago, Joe Ajaero zai amsa gayyatar ƴan sanda domin amsa wasu tambayoyi game da zarginsa da ɗaukar nauyin ta’addanci da laifukan kafofin sadarwa da cin amanar ƙasa da sauransu.
Ƴan sanda dai sun gayyaci shi ne bayan wani samame da suka kai a sakatariyar NLC da ke Abuja.
“Ƴan sandan sun ce sun yi samamen ne domin gano wasu muhimman abubuwa da suke da alaƙa da zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi a Najeriya,”
Domin nuna goyon baya ga Ajaero, Ƙungiyar Ƙwadago ta umarci mambobinta a faɗin ƙasar da su taru a hedkwatar ƴan sanda na jihohinsu, “har sai shugabansu ya bar hedkwatar ƴan sandan.”
Idan ba a manta ba, dubban mutane ne suka fito suka yi zanga-zangar matsin rayuwa, ƙarƙashin jagorancin wata ƙungiya mai suna Coalition of Concerned Nigerian Citizens.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 1 minute 23 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 42 minutes 48 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com