Shugaban ƙungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, bisa rakiyar ƴan ƙungiyar ƙwadago da Femi Falana, lauyoyi da suka haɗ da Femi Falana lauya mai rajin kare hakkin ɗanadam a Najeriya da Deji Adeyanju, ya gana da ƴansanda a hedikwatarsu da ke babban birnin tarayya domin amsa gayyatar suka yi masa.
Rundunar ‘yan sandan dai ta gayyaci shugaban NLC ɗin ne bisa zargin sa da tallafa wa ayyukan ta’addanci, wanda shugaban da ƙungiyar suka musanta.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Tun da karfe takwas na safe ne shugabannin NLC ɗin suka fara hallara a hedikwatarsu, inda suka gudanar da gangamin nuna hadin kai da goyon baya ga Ajaero.
Bidiyon da aka wallafa a shafin sada zumuntar NLC na X sun nuna wasu shugabannin kwadagon suna jawabi ga ma’aikatan da suka taru, wadanda suka tsaya kyam a bayan Shugaban nasu.
Kawo yanzu dai babu cikakken bayani na haƙiƙanin abin da ya faru a yayin ganawar.
Tun da farko dai ‘yan sandan sun gayyaci Ajaero a makon da ya gabata, bisa zargin bayar da kudade ga ayyukan ta’addanci, da cin amanar kasa, da kuma aikata laifuka ta shafukan sada zumunta.












