Home General Sojojin Saman Nijeriya sun hallaka ‘yan bindiga 5 a jihar Kaduna

Sojojin Saman Nijeriya sun hallaka ‘yan bindiga 5 a jihar Kaduna

Dakarun sojojin saman Nijeriya sun sami nasarar halaka jagoran ‘Yan ta’addan da ya addabi al’umma a jihar Kaduna Mustapha Abdullahi, da wasu yaran sa biyar a karamar hukumar Igabi dake jihar.

Daraktan yada labaran rundunar sojin AVM Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar lahadi, in da ya ce dakarun da rundunar sojin ta 413 ne suka sami nasarar kan gungun ‘yan ta’addan.

Sanarwar ta ce yayi da suke aiki da bayanan sirrin da suka samu dakarun na musamman da aka girke a dajin Sabon Gida, a kokarin da suke na kakkabe ayyukan ‘yan Ta’addan dake addabar Al’umma suka sami damar tarwatsa gungun ‘yan bindigar.

A yayin atisayen sojojin sun sami nasarar kwato makamai masu tarin yawa da suka hadar da bindiga kirar gida guda biyar, da wata babbar binidga kirar gida guda daya, sai kuma alburusai masu tarin yawa da sauran makamai.

Gabkwet yace ‘yan ta’addan nada aniyar aikata garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, cutarwa gami da hallaka fararen hula da basu ji ba basu gani ba.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp