Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarawa Babban Sefotun ‘yan sandan kasar Kayode Egbetokun wa’adi, kamar yadda wata majiya daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta bayyana.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito an ƙara wa shugaban ‘yan sandan wa’adin shekara uku ne, ma’ana sai zuwa 2027.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ta ruwaito cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ne ya bai wa Babban Sufeton ‘yan sandan takartar ƙara masa wa’adin a ranar Litinin.
A watan Yulin da ya gabata ne Majalisar Dattijan Najeriya ta yi garambawul ga dokar ‘yan sanda ta 2020 ƙarƙashin sashe na 8, wadda ta ci karo da ƙarawa ma’aikacin gwamnati wa’adin aiki bayan shekara 35 ko kuma bayan kaiwa shekara 60 a raye.
Egbetokun wanda aka naɗa IG a watan Yunin 2023 zai cika shekara 60 ne a gobe 4 ga watan Satumba.











