Kamfanin NNPCL ya kara farashin litar Mai a Nijeriya

Kamfanin mai na Nijeriya, NNPCL ya sanar da sabon farashin litar man fetir. A wata sanarwa da kamfanin ya aike wa manema labarai, kamfanin ya ce daga yau ranar 3 ga watan Satumban 2024, kamfanin ya ƙara kuɗin litar man fetir daga naira 617 zuwa 897.

Tuni dai wasu gidajen Mai a Nijeriya suka sauya farashin litar zuwa sabon da kamfanin ya sanar a ranar ta Talata.

Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan da kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa yana fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi, wani abu da ya sa ƴan Nijeriya hasashen kamfanin na koƙarin sanar da sabon farashi ne.

Da ma dai kafin sanar da sabon farashin na ranar Talata, dogayen layukan ababan hawa sun mamaye gidajen mai a biranen Abuja da Legas.

Tun dai bayan da gwamnatin shugaba Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ƴan Nijeriya ke fuskantar sauye-sauye a farashin man wanda kuma ke taɓa sauran sassan rayuwa.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1189 days 15 hours 24 minutes 22 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1171 days 17 hours 5 minutes 47 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com