Home General Sojojin Najeriya sun kama masu kai wa ‘yan bindiga makamai a kasar

Sojojin Najeriya sun kama masu kai wa ‘yan bindiga makamai a kasar

Wasu rahotannin daga Nijeriya na bayyana cewa dakarun Sojojin kasar tare da takwarorinsu na tsaro sun kama wasu mutane 15 da ake zargi da samar wa ‘yan bindiga makamai da sauran kayan aiki.

Wannan na cikin wata sanarwa da sojojin suka wallafa a shafinsu na X, inda suka ce an yi kamen ne bayan samun bayanan sirri kan mutane.

Sanarwar ta ƙara da cewa an kashe wani mutum guda da ake zargin ɗan bindiga ne yayin wannan samamen a wurare da dama.

A yayin saman dakarun kasar sun yi nasarar kama makamai masu dama da alburusai da kuma wasu kayayyaki na daban.

“A ranar 30 ga watan Agusta 2024, dakaru sun kai hari kan ‘yan bindiga da masu yi musu jigilar kayayyakinsu a Mararaba Donga da ƙauyen Manya da suke a Ƙananan hukumomin Donga da Takum a jihar Taraba.

“An kama mutum biyar da ake zargi a lokacin samamen, an kuma kamaya kayayyaki kamar haka: bindiga uku ƙirar AK-47, bindiga biyu ƙirar cikin gida, bindiga biyu ƙirar da ba ta gida ba, bindiga biyu ta farauta, wata bindiga mai ɗaukar harsashi 61 da dai sauransu.

“A Yobe dakarun sun kama wasu masu kaiwa mayaƙan Boko Haram kayan aiki a ƙauyen Jimbal da ke ƙaramar Hukumar Tarmuwa.

“A Kaduna an kama makamantan waɗannan mutane masu kai kayan aiki a ƙauyen Rijana a ƙaramar Hukumar Chikun. Tare da su akwai wayoyi uku da ke da katin waya sama da naira 100,000, an kuma samun garin kuɗi naira 1,532,900.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp