Annobar amai da gudawa ta hallaka mutane bakwai a jihar Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa dake arewa Maso yammacin kasar ta tabbata da barkewar annobar amai da gudawa a karamar hukumar kirikasamma, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai tare da kwantar da dama a Asibitin jihar.

Shugaban kula da lafiyar al’umma na yankin na kirikasamma, Musa Abdullahi Diladige ne, ya tabbatar da barkewar cutar a yankunan Malori, Maikintari, Dilmari, Kirikasamma, da wani bangare na kauyen Baturiya.

Diladige, ya bayyana cewa wadanda abin ya shafa na fama da alamomin rashin lafiya masu tsanani kamar gudawa, kumburin ciki, amai, da zazzabi

An tura ma’aikatan lafiya zuwa yankunan don samar da agajin gaggawa.

Hukumomi sun dauki matakin gaggawa ta hanyar sayan magungunan da ake bukata don fara jinyar masu cutar.

Daraktan gudanarwa da ayyukan gama-gari, Idris Gambo Abubakar, ya yi alkawarin bayar da goyon bayan da ake bukata don dakile yaduwar cutar.

Ana kyautata zaton ruwan sama mai tsanani da aka samu a yankin ne ya haifar da barkewar cutar, inda gine-gine suka lalace kuma hanyoyin samar da ruwa suka lalace.

An shawarci mazauna yankin da su dauki matakan kariya nan take.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com