Home General Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta yi Allah-wadai da karin farashin Man Fetur

Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta yi Allah-wadai da karin farashin Man Fetur

Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Nijeriya tayi Allah wadai tareda nuna rashin Jin dadinta bisa tashin gwauron zabi da man fetur yayi a fadin Kasar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kungiyar ta fitar  bayan da kamfanin Man Fitor na kasar NNPCL ya fitar da sanarwar Kara farashin Man fetur.

Sanarwar da Sakataren Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa Shehu Tasiu Ishaq da sakataren yada labarai na Kungiyar Abubakar Balarabe Kofar Naisa suka sanyawa hannu tace bisa la’akari da halin da ‘Yan kasa ke ciki akwai bukatar a duba lamarin.

Kungiyar ta bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rage farashin Man fetur din a maimakon Kara farashin sa, domin saukakawa al’ummar Nijeriya.

Daga bisani sanarwar ta bukaci al’ummar kasar su cigaba da yin addu’oi na neman samun sassaucin al’amura da samun cikakken tsaro da wadatar arziki a Kasa baki daya.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp