Majalisar jihar Kano ta Amince da kudirin kara kasafin kudin jihar

Majalisar jihar Kano
Majalisar jihar Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kudirin kara kasafin kudin jihar da naira biliyan 99.2

Kudirin ya samu karbuwa daga dukkan kwamitin majalisar baki daya bayan kammala karatu na uku a zauren majalisar a ranar Alhamis.

Gwamna Abba Yusuf ya gabatar da kudirin dokar ne a ranar 26 ga Agusta, 2024 inda ya nemi a kara kasafin kudin zuwa Naira biliyan 536, 559, 816, 357.84 maimakon Naira biliyan 437, 338, 312, 787 da aka sanya wa hannu a watan Disamba 2023.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala zaman majalisar, shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Hon. Aminu Sa’ad, ya bayyana cewa, kashi 58 cikin 100 na kasafin kudin an ware su ne domin manyan ayyuka na more rayuwa yayin da kashi 42 cikin 100 kuma aka ware domin gudanar da ayyukan yau da kullum.

Hon. Sa’ad ya kara da cewa, karin kasafin kudin an yi shi ne domin aiwatar da zabukan kananan hukumomi da ke tafe, biyan sabon mafi karancin albashi, kudaden gudanarwa ga sabbin ma’aikatun da aka kafa da sake bude cibiyoyin koyar da sana’o’i da sauran ayyukan da gwamnati ta sa gaba.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 19 minutes 27 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 52 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com