Home General Dalilin da ya sa Ajuri Ngelale Ya ajje mukamin sa

Dalilin da ya sa Ajuri Ngelale Ya ajje mukamin sa

Mai bai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ajuri Ngelale, ya tafi hutun sai baba ta gani saboda rashin lafiya ba tare da shiri ba.

Ngelale ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne bayan shawarwari da iyalinsa suka ba shi, saboda wani mummunan yanayi na rashin lafiya da ya ƙara ta’azzara masa.

Ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya aikewa Shugaban Ma’aikatan Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, a yau Asabar.

Ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan tuntuɓar iyalinsa saboda yanayin rashin lafiyar da ke ƙara tsananta, kuma hakan ya sa dole ya dakatar da aikinsa na Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yada Labarai da sauran mukamansa.

Ngelale ya ƙara da cewa yana fatan dawowa bakin aikinsa idan ya samu waraka, idan kuma yanayi ya bayar da dama, sannan ya roki a bar shi shi da iyalinsa damar samun zaman lafiya a tsawon wannan lokacin.

Wannan hutun yana nufin zai dakatar da aikinsa na mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu na tsawon lokacin da zai ɗebe yana jinyar.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp