Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nuna matukar damuwarsa game da ambaliyar ruwa da ta afku a wasu sassan Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar.
Ambaliyar ruwan ita ce mafi muni a cikin shekarun baya-bayan nan da birnin ya fuskanta yayin da ta raba dubban mutane da muhallansu tare da yin ɓarna a karamar ofishin gidan waya da asibitin koyarwa na Maiduguri.
Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar, musamman waɗanda suka yi asara sakamakon bala’in da ambaliyar ruwan ta haddasa.
Tinubu ya kuma yi kira da a gaggauta kwashe mutane daga yankunan da abin ya shafa yayin da hukumomi ke ci gaba da tantance irin ɓarnar da ambaliyar ta yi.
Shugaban ya kuma umurci hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) da ta taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 43 minutes 3 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 24 minutes 28 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com