Home General Sojojin Najeriya sun hallaka kwamanda ISWAP “Ibn Kaseer” a Borno

Sojojin Najeriya sun hallaka kwamanda ISWAP “Ibn Kaseer” a Borno

Dakarun sojin Nijeirya karkashin  rundunar Operation hadin kai ta sami nasarar hallaka kwamandan mayakan kungiyar ISWAP, Ibn Kaseer tare da wasu mayakan kungiyar guda uku a wani hari da suka kai dajin Sambisa a safiyar ranar Alhamis.

Zagazola makama ya bayyana cewa wani rahoton sirri ya tabbatar da yadda dakarun sojojin karkashin rundunar sojoji ta 21, sun sami nasarar a yayin wata kora da suka kai a kauyen Kashomeri.

Kwamandan mayakan na ISWAP ta ya addabi al’ummar Geizuwa da Yale ya yi yunkurin samun mafaka a yankin na Kashomeri shi da iyalansa.

Majiyar dai ta tabbatar da cewa bayan bankado maboyar ta sa ne dakarun suka hallaka shi tare da wasu mayakansa guda biyu da aka bayyana a matsayin Bulamadu, sai dai majiyar tace lamarin ya faru ne bayan da mutanen sa suka fita wani aikin taaddanci a yankin Jalumeri.

Haka kuma bayan hallaka kwamandan rundunar ta sami nasarar kubutar da mata hudu da yara kanana, yayin da wasu daga cikin ‘iyalan mayakan na ISWAP suka mika wuya ga dakarun sojojin a Kunduga.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp