Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC ta ce za ta sake komawa ga gwamnatin tarayya domin ta ji yadda ma’aikata za su rayu bayan sake kara farashin man fetur a kasar.
Kungiyar ta kwadago ta bayyana hakan a ranar Alhamis in da ta ce farashin mai a yanzu haka ya riga ya haɗiye sabon tsarin albashin da gwamnati ta yi alƙawarin bayarwa na naira dubu 70 wanda kuma har yanzu ba a fara bayarwa ba.
Shugaban ƙungiyar ta NLC, Kwamared Joe Ajaero wanda ya bayyana hakan yayin buɗe wani taron ƙarawa juna sani a Legas ya ce gwamnati ta yaudare su ta hanyar amince wa da naira 70,000 ɗin a matsayin albashi mafi ƙaƙanta.
Ya kuma shawarci gwamnati da ta magance matsalar yunwa da talauci da damuwar da ƴan Najeriya ke fama da ita tun kafin al’amura su fi ƙarfinsu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 29 minutes 47 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 11 minutes 12 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com