Gwamnatin Kano ta samu bashin Naira biliyan 177.4 daga Hukumar Cigaban Faransa wato French Development Agency domin samar da ruwan sha a jihar.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Ruwa na jihar, Alhaji Ali Haruna Makoɗa ya wakilta ne ya bayyana hakan a wani taron ƙara wa juna sani na kwanaki biyu da aka yi a Kano domin bibiya da tsara aikace-aikace wanda ya samu halartar wakilai daga jihohin Filato da Enugu da Ondo.
Ya ce aikin na samar da ruwan sha, yana cikin shirin inganta samar da ruwan sha na ƙasa, wanda ya samu sahalewar Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Najeriya.
Gwamnan ya ce an samu tsaiko ne a kan aikin ne tun bayan ɓarkewar annobar COVID-19 da wasu ƙalubalen, amma ya ƙara da cewa yanzu sun shirya cigaba da aikin, wanda ya ce za a kammala nan da shekara biyu.
Injiniya Garba Ahmad Bichi, Manajan Darakta na Hukumar Gidan Ruwan Kano ya ce aikin ya ƙunshi sake gina sabon hanyar adanawa da gyara ruwa wanda zai ɗauki lita miliyan 250 a kullum, wanda ya ce zai taimaka matuƙa wajen rage matsalar ƙarancin ruwa a jihar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 3 minutes 14 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 44 minutes 39 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com