Yan jarida 128 ne aka kashe a yaƙin Isra’ila da Hamas – CPJ

Shekara guda da fara yaƙi tsakanin Hamas da Isra’ila, ƙasar ta Yahudawa ta kashe ƴan jarida da ma’aikatan kafafen yada labarai da yawan su ya zarce yadda aka taɓa gani.

ta cikin wani jawabi da kungiyar kare hakkin ‘yan jaridu ta duniya CPJ tace tun da ta fara ajiyar bayanai a game da yan jarida da ake kashewa daga shekarar 1992 bata taba samun kamar na wannan yaki ba.

CPJ ta ce aƙalla yan jarida da ma’aikatan kafafen yaɗa labarai 128 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kai wa  Gaza, kuma daga cikinsu, biyu ne kawai za a ce babu hannun dakarun Isra’ila a mutuwarsu.

Ƙungiyar CPJ ta gano cewa da gangan Isra’ila ta kashe yan jarida aƙalla 5  saboda ayyukan da su ke gudanarwa, kuma tana ci gaba da bincike a game yiwuwar kisan wasu ƴan jarida 10 da gangan.

A ranar 7 ga watan Oktoban bara, ƴan jarida, ƴan asalin Isra’ila sun mutu sakamakon harin da mayaƙan Hamas su ka kai ƙasar, wanda ya haddasa yaƙin da ake ci gaba da yi a halin yanzu.

Kasashe-kashen da katsalandan a cikin aikin jarida, kame da kuma katse layukan intanet  da lalata gidajen jarida da sauran su, sun haddasa tasgaro a aikin aikewa da rahotanni a ,game da abubuwan da ke faruwa a Gaza. Sai dai daga rana r 4 ga watan Oktoba, CPJ ta tabbbatar da wadannan cewa:

Daga cikin yan jarida 128 da aka kashe, 123 Falasɗinawa ne, sai ƴan Lebanon 3  da ƴan Isra’ila 2.

Kashi 11 na waɗanda aka kashe, mata ne,kuma akasarin ƴan jaridan da aka kashe ba su na ƙasa da shekaru 40 da haihuwa.

Hare-haen sama da Isra’ila ta kai ne su ka yi sanadin mutuwar Kashi 75 na Falasɗinawa ƴan jarida; sauran sun mutu ne sakamakon harbi da su ka hada da na jirage marasa matuƙa, tankokin yaƙi da sauransu.

Tun da aka fara yakin, an kama Falaɗinawa yan jarida 69; Isra’ila ta kame 66, sai makuntan Falasɗinu sun kama 3. Har yanzu akwai Falasdinawa yan jarida guda 43 da ke tsare a hannun mahukuntan Isra’ila.

An samu rahoton lalata  gidajen jarida kimanin 70 a wannan yaƙin, kana Isra’ilar ta rufe wasu 5 har sai illa masha allahu.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 6 hours 34 minutes 1 second,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 8 hours 15 minutes 26 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com