Jam’iyyar APC mai mulki ta ce bata tsorata ba da yunkurin kulla kawance tsakananin Rabi’u Musa Kwakwanso na NNPP da Peter Obi na LP a yayin da ake tunkarar zaben shugaban kasa na 2027.
A yayin ganawa da jaridar The PUNCH a ranar Litinin, daraktan yada labarai na APC, Bala Ibrahim ya bayyana cewa yunkurin kawance tsakanin Kwankwaso da Obi ba zai nasara ba kamar yadda ya faru a zaben 2023.
Read Also:
Acewarsa, rashin amincewa tsakanin Obi da Kwankwaso zai zama cikas gare su, kuma duk a cikin su ba wanda zai hakura ya bar wa wani takarar shugaban kasa.
tun da fari dai an hangi Kwankwaso na cewa bashi da matsala idan an ce ya yiwa Obi mataimaki, amma azo a duba waye ya fi chanchanta, duk da cewar dai da dama cikin jaridun Nijeriya sun yiwa kalaman nasa bahaguwar fahimta
Da yake mayar da martani a ranar Litinin, Sakataren jam’iyyar LP, Umar Faruk ya yi maraba da damar da Kwankwaso ya bayar, inda ya ce majar za ta yiwuwa idan Kwankwaso ya amince zai yi aiki da Obi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 1 hour 48 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 3 hours 30 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com