Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shawarci tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawan ƙasar, Sanata Ali Ndume kan ya riƙa gabatar da ƙorafin sa kai tsaye ga shugaba Bola Tinubu, a madadin fita fili yana sukar tsare-tsaren gwamnati.
Daraktan yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Bala Ibrahim ne ya bayyana hakan ga manema labarai inda ya ce kowanne ɗan ƙasa yana da ƴancin bayyana ra’ayin sa a tsarin dimokuraɗiyya, amma akwai buƙatar manyan ƴan siyasa irin su Ndume su riƙa kiyaye irin bayanan da zasu yi a bainar jama’a.
Sanata Ndume mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya ya bayyana a cikin shirin Ra’ayi Riga na BBC Hausa, inda ya buƙaci gwamnatin shugaba Tinubu ta ɗauki matakan kawo sauƙin halin matsi da ƴan Najeriya ke ciki, ya yi kiran a dakatar da ƙarin farashin mai a ƙasar.
Sanata Ndume ya kuma fitar da wata sanarwa ga manema labarai domin jaddada matsayar sa a kan halin da ake ciki, inda ya yi iƙirarin cewa akwai wasu da ke tunzura gwamnati tana aiwatar da tsare-tsare masu tsauri.
A watannin baya ma jam’iyyar APC ta nemi majalisar dattawa ta ladabtar da Sanata Ndume ta hanyar ƙwace mukamin sa na mai tsawatarwa saboda yadda ya ke fita kafafen yaɗa labarai yana sukar gwamnatin APC.
Daga baya sanatan ya nemi afuwa kuma jam’iyyar ta yafe masa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 58 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 40 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com