Home Labarai Bukola Saraki ya taya wankwaso murnar cika shekaru 68

Bukola Saraki ya taya wankwaso murnar cika shekaru 68

Tsohon shugaban majalisar dattawa ta ƙasa, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya ce tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kwararre ne wajen iya jagoranci.

Saraki ya bayyana haka ne a saƙon taya Kwankwaso murnar cika shekara 68 da haihuwa a yau 21-10-2020.

A cikin wata sanarwa da mataimakinsa a kan kafafen yada labarai, Abba Gwale ya fitar, Saraki, ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan uwa kuma aboki wanda kuma ya kware wajen iya jagoranci.

 

“Abokina kuma ɗan uwana, tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kasance ƙwararren ɗan siyasa kuma jagora na gari.

 

“A yau da yake murnar zagayowar ranar haihuwarsa, ina taya iyalansa da ƴan uwansa da mabiyansa murnar wannan rana, sannan ina roƙon Allah ya ci gaba da ƙarfafa masa gwiwa, ya bashi cikakkiyar lafiya da basira da tsawon rai”. Inji Saraki.

Saraki da Kwankwaso dai sun yi aiki tare a majalisa ta takwas, a lokacin da Sarakin, wanda shima tsohon gwamnan jihar Kwara ne, yake matsayin shugaban majalisar dattawa daga shekara ta 2015 zuwa 2019, lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp