Home Labarai Gwamna Kano ya taya Kwankwaso murna cika shekaru 68 a duniya

Gwamna Kano ya taya Kwankwaso murna cika shekaru 68 a duniya

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf taya mai gidansa sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 68 a duniya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikewa manema labarai a jihar.

Cikin Wani Sako da Gwamnan ya Wallafa a Shafinsa na Sada zumunta Wanda ya dauki hankali Al’umma musamman Yan Siyasa dake Tabbatar da biyayya ga Mai Gidansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

“Ya zama wajibi na mika sakon Taya murna kasancewar ka a matsayin jagora kuma shugaba wanda na yi aiki da kai tsawon shekaru 38 da suka wuce”. Inji Gwamnan

Gwamnan ya kara da cewa “lokacin da na yi aiki da Kwankwaso na koyi abubawa da dama wadanda suka taimake ni a Rayuwa dan haka na ke mika sakon taya Murnar zagayowar ranar haihuwar Mai gidana Shekaru 68 a Duniya”.

Kwankwaso Wani jigo ne a Siyasa a Kasar nan Wanda Yake da Wasu Muhimman abubuwan koyi na Cigaba ga Al’ummar Kasar nan a cewar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya ce a madadin shi Kansa da iyalansa, gwamnati da al’ummar jihar Kano yana taya tsohon gwamnan murnar cika shekaru 68 a duniya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp