Gwamnatin Najeriya ta sanar da kawo ƙarshen yarjejeniyar aikin hanyar da ta tashi daga Abuja zuwa Kaduna da ta ƙulla da kamfanin Julius Berger.
Bayan cikar wa’adin kwanaki 14 da gwamnatin ta baiwa kamfanin na ɗaukar mataki kan tafiyar wahainiya da aikin ke yi, a yanzu ta sanar da ficewa daga yarjejeniyar ba tare da samun damar yin wata tattaunawa ba.
Read Also:
Ta cikin sanarwar da ma’aikatar ayyukan ta fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaranta Mohammed Ahmed ta ce an shafe watanni 13 a jere ana tattaunawa da kamfanin amma an kasa cimma matsaya, don haka babu wani zabi da ya wuce kawo ƙarshen yarjejeniyar.
Baya ga tafiyar wahainiya da aikin ke yi, ana kuma zargin sa da ƙin bada cikakken bayani kan kuɗin da aikin ya laƙume kawo yanzu, ƙin biyayya ga dokokin da aka shimfida, da kuma ƙin biyayya ga shawarwarin da ma’aikatar ayyuka ta bashi.
RFI ta ruwaito cewa an shafe tsahon watanni ana yamutsa gashin baki tsakanin kamfani da gwamnati kan waɗannan matsaloli da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 8 minutes 55 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 50 minutes 20 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com