Shugaba Tinubu ya isa Saudiyya don taro kan rikicin Gabas ta Tsakiya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauƙa a Riyadh, babban birnin Saudi Arabia, a yau Lahadi domun halartar taron ƙoli na ƙasashen Larabawa da Musulmi da za a fara gobe Litinin, 11 ga watan Nuwamba, 2024.

Za a yi taron ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bayan makamancin taron da aka yi a birnin a bara.

Taron zai mayar da hankali ne kan halin da ake ciki yanzu a Gabas ta Tsakiya.

A sanarwara da mai bai wa shugaban shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayar ya ce Tinubun yana tare da ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris da kuma shugaban hukumar bayanan sirri ta Najeriya, Mohammed Mohammed.

Sanarwar ta ce ana sa ran a wajen taron Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi a kan rikicin Isra’ila da Falasdinawa, inda zai jaddada matsayar Najeriya ta neman sasanta rikicin ta hanyar dakatar da bude wuta nan take, tare da neman a sake farfaɗo da masalahar samar da ƙasashe biyu masu ciin gasin kansu – wato Falasɗinu da Isra’ila.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 11 hours 18 minutes 17 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 59 minutes 42 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com