Yahaya Bello ya musanta zargin rashawa a gaban kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello tare da wasu mutane biyu da Hukumar EFCC ta gurfanar a gaban kotu a yau Laraba sun musanta zarge-zargen rashawa na Naira biliyan 80 da ake yi musu.

Yahaya Bello, wanda shi ne na farko a cikin mutanen da ake tuhuma tare da sauran mutanen biyu Shuaibu Oricha da Abdulsalami Hudu, sun musanta duka tuhuma 16 da aka fara karanto musu a gaban mai shari’a Maryanne Anenih ta babbar kotun ta Abuja.

Joseph Daudu, (SAN) shi ne jagoran lauyoyin da ke kare toshon gwamnan da sauran waɗanda ake tuhuma, yayin da Kemi Pinhero (SAN), ke jagorantar masu gabatar da ƙara.

Bayan musanta aikata laifukan, lauyan waɗanda ake tuhumar ya nemi a bayar da belin Bello amma lauyan EFCC ya nemi kada a bayar da cewa wa’adi ya wuce tun watan Oktoba.

To amma bayan sauraron ɓangarorin biyu kotun ta tsayar da ranar 10 ga watan Disamba mai kamawa domin duba buƙatar belin.

EFCC ta yi nasarar gurfanar da tsohon gwamnan na jihar ta Kogi a gaban kotun ta tarayya da ke Abuja a yau Laraba bayan wata da watanni na gaza hakan, kasancewar ya ƙi amsa gayyatar hukumar kuma duk yunƙurinta na kama shi ya ci tura.

A ranar Talata ne aka ce tsohon gwamnan ya kai kanshi hukumar ta EFCC da rakiyar lauyoyinsa – amma daga baya hukumar ta ce tana tsare da shi.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 4 hours 21 minutes 44 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1444 days 6 hours 3 minutes 9 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com