Rundunar Sojojin saman Nijeriya ta tabbatar da kudirinta na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali da zaman lafiya a fadin kasar, gami da samar da kayan yaki ga dakarun sojojin dake bakin daga.
wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran shalkwatar rundunar sojojin saman kasar Air Commodore Olusola F Akinboyewa ya aikewa PRNigeria mai dauke da kwanan watan 27 November 2024.
sanarwar ta kara da cewa dakarun ta sun sami nasarar kai wasu gwamman hare hare mabambanta a garin kukawa dake jihar borno a arewa maso gabashin Nijeriya kan mayaka masu tada kayar bayawa.
Read Also:
harin wanda dakarun sojojin saman karkashin rundunar Operation HADIN KAI (AC OPHK) su kai kan mayaka masu tada kayar baya ya tarwatsa maboyar mayakan.
harin farko da sojojin suka kai sa faru ne bisa wasu bayanan sirri da suka samu, kan maboyar motar yakin ‘yan ta’addan a arewacin kukawa dake da nisan kilomita 5 a jihar borno, nan take dakrun sojojin suka kai dauki inda suka sami nasarar tarwatsa su.
hari na biyu da dakrun suka kai garin na kukawa sun kai shi ne bayan sun sami kira daga kauyen cewa wasu mahara bisa babura sun kai musu hari, nan tyake dakraun sojojin suka kai dauki.
bayan musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan ta’addan dakrun sojojin sun sami nasarar halaka da dama daga cikin su, inda suka kwace babura 20 daga hannun ‘yan ta’addan bayan guduwa da suka yi daji da raunikan harbin bindiga a jukkunan su.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1462 days 9 hours 24 minutes 32 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1444 days 11 hours 5 minutes 57 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com