Kwale kwale ya kife da mutane da dama a jihar Neja

Rahotannin daga jihar Neja na bayyana cewa a safiyar yau Juma’a ce aka wayi gari da kifewar wani kwale-kwale a sashen Dambo-Ebuchi na tekun Neja, wanda ya yi sanadiyar wasu mutane.

Waɗanda lamarin ya auku a gaban su sun shaida wa tashar Channels cewa, kwale-kwalen, wanda na wani mai suna Musa Dangana ne, yana tafe ne da fasinjoji sama da 200, ciki har da mata ƴankasuwa da masu aikin gona waɗanda za su tafi kasuwar mako-mako ta Katcha.

A watan Oktoba ne aka samu kwatankwacin hatsarin nan a kwale-kwale a rafin Muwo Gbajibo da ƙaramar hukumar Mokwa na jihar ta Neja, inda mutane da dama suka rasu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com