Home General Tinubu ya yaba da sake zaɓar Ngozi shugabar WTO

Tinubu ya yaba da sake zaɓar Ngozi shugabar WTO

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya – shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya, (WTO) Dakta Ngozi Okonjo-Iweala – murnar sake zaɓarta a muƙamin a wa’adin mulki na biyu.

A ranar Juma’a ne aka sake zaɓar Dakta Ngozi a matsayin shugabar WTO a wa’adin mulki na biyu.

Cikin wata sanarwar da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya ce ya yi farin ciki da yadda ƙasashe mambobin WTO suka amince wa Ms Okonjo-Iweala ta zarce a karo na biyu na shugabancin WTO.

”Hakan ya nuna irin ƙwarin gwiwa da amincewa da duniya ta yi da jagorancinta, tare da cike da fatan ƙarfafa da bunƙasa kasuwancin duniya”, in ji Tinubu.

A shekarar 2021 ne tsohuwar ministar ta Najeriya – wanda kuma fitacciyar masaniyar tattalin arziki da kuɗaɗe ce – ta kafa ta tarihin zama ‘yar Afirka ta farko kuma mace ta farko da ta taɓa jarogantar ƙungiyar WTO mai mambobin ƙasashe 164 a faɗin duniya.

Wa’adin mulkinta na farko a matsayin shugabar WTO ta bakwai zai ƙare ranar 31 ga watan Agustan 2025, yayin da wa’adinta na biyu zai ƙare a shekarar 2029.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp