Home General Nijeriya da Afirka ta kudu sun sake kulla kyakkayawar alaka

Nijeriya da Afirka ta kudu sun sake kulla kyakkayawar alaka

kasashen Najeriya da Afirka ta kudu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin haɗin gwiwa a ɓangaren kasuwanci, tattalin arziƙi da kuma tsaro, inda shugaba Cyril Ramaphosa ya amince da fara bai wa ƴan Najeriya musamman ƴan kasuwa damar samun bizar ƙasar ta shekaru 5, ba tare da nuna fasfo ba.

Ramaphosa ya bayyana wannan mataki a matsayin wani ɓangare na ƙara ƙarfafa alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu, lokacin buɗe taron hukumar haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu karo na 11 a birnin Cape Town na ƙasar .

Shugaba Ramaphosa ya ce hakan zai sauƙaƙa tafiye-tafiyen ƴan kasuwa da masu yawon buɗe ido zuwa ƙasar, ta hanyar samun bizar shekaru 5 fiye da sau 1.

Cyril ya yi alƙawarin cewa Afirka ta kudu za ta cire ka’idoji kan sanya hannun jari, tare da magance matsalolin da kamfanoni ke fuskanta na ƙasashen biyu.

A bayanin bayan taro da suka fitar ya nuna cewa, ƙasashen biyu sun ƙarƙare tattaunawar kan yarjejeniyar shekaru 5 ta musayar bayanai akan matsaloli na aikata manyan laifuka, barazanar tayar da hatsaniya, da kuma cin zarafi ƴa ƴan ƙasashen.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp