Home General An sake samun daukewar babban layin wutar lantarki a Najeriya

An sake samun daukewar babban layin wutar lantarki a Najeriya

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ofishin dake kula da babban layin wutar lantarki a Najeriya, ya ce layin ya sake daukewa da misalin karfe 2 da minti tara na rana agogon kasar a ranar Laraba.

Cikin sakon, ofishin ya ce tuni aka fara kokarin dawo da layin bakin aiki.

Daukewar babban layin wutar lantarkin da ake yawan samu a kasar, na janyo babbar asara musamman ga ‘yan kasuwa wadanda ke neman kudi ta hanyar amfani da lantarki.

Ofishin, ya nemi afuwar al’ummar Najeriya, yana mai cewa tuni aka dukufa don dawo da wutar.

An samu daukewar babban layin wutar lantarkin sau 12 ke nan tun daga farkon shekarar 2024 kawo yanzu.

Babban layin wutar lantarki na Najeriya – power grid a Turance – gungun layuka ne da suka haɗa tashoshin samar da lantarki da ke bai wa dukkan sassan Najeriya wuta.

A taƙaice, wata ma’dana ce da ke ɗauke da dukkan lantarkin da ake sha a Najeriya. Haka nan, ba wani wuri ba ne guda ɗaya, tarin layuka ne a wurare daban-daban.

An tsara shi ne don ya yi aiki ta wasu taƙaitattun hanyoyi musamman dangane da yawan wutar da ake da ita, da tsaron lafiyarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp