Home General Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur zuwa ₦899

Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur zuwa ₦899

Matatar mai ta Dangote ta ce ta rage farashin litar man fetir zuwa naira 899.50 gabanin bikin kirsimati da sabuwar shekara.

Kakakin matatar Anthony Chiejina, ya ce an rage farashin litar man ne domin rage tsadar sufuri ga jama’a, a lokacin shagulgulan ƙarshen shekara.

A cikin watan Nuwamba ma, matatar man mai zaman kanta ta rage farashin litar mai zuwa naira 970.

Ya ce “Domin samar da sauƙi kan sufuri a lokacin hutun ƙarshen shekara, matatar mai ta Dangote ta fara sayar da mai a kan ragin farashi. Daga yau za a riƙa sayar da man a kan naira 899.50 a kowacce lita, daga mtatar man tamu.”

Chiejina ya jaddada cewa matatar ta jajirce wajen tabbatar da ganin an samarwa jama’ar Najeriya man fetir mai inganci kuma cikin farashi marar tsada.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp