Home General ‘Yanmajalisar wakilan Najeriya sun tara miliyan 704.91 daga albashinsu don tallafa wa...

‘Yanmajalisar wakilan Najeriya sun tara miliyan 704.91 daga albashinsu don tallafa wa ‘yan ƙasa

‘Yanmajalisar Wakilan Najeriya za su gabatar wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kuɗin da suka tara daga albashinsu domin ba da tasu gudummawar wajen rage wa ‘yan Najeriya tsadar rayuwa.

Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas ne ya bayyana hakan yayin zaman majalaisar a yau Alhamis, yana mai cewa kuɗin sun kai naira miliyan 704.91.

Ya ce za su yi hakan ne a ranar 31 ga watan Disamban 2024. Tun a watan Yuli ne ‘yanmajalisar suka yi alƙawarin sadaukar da rabin albashinsu domin taimakawa saboda cire tallafin man fetur.

“Ina farin cikin shaida muku cewa zuwa yanzu mun tara naira N704,907,578.82,” in ji Tajudeen.

“A ranar 31 ga watan Disamba, zan jagoranci shugabannin majalisa domin kai wa shugaban ƙasa kuɗin da zimmar yin amfani da su wajen tallafa wa mabuƙata.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp