Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce ba ya nadamar cire tallafin man fetur da ya yi a farkon kama mulkinsa.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Litinin da daddare, a tattaunawarsa ta farko da kafafen yaɗa labaru tun bayan hawa mulkin Najeriya a watan Mayun 2023.
Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da aka yi masa tambaya kan ‘ko da ya fi kyau idan an jinkirta cire tallafin man fetur da kuma barin kasuwa ta tantance darajar naira’.
Tinubu ya ce “babu yadda za a yi na bari ana sayar da man fetur ta yadda ƙasashe maƙwafta za su riƙa samun garaɓasa. Ba na nadamar komai game da cire tallafin man fetur.
Read Also:
”Muna kashe abin da za mu amfana da shi a gaba ne, muna yaudarar kanmu ne kawai, wannan sauyi dole ne, ” in ji shi.
Sannan ya kara da cewa shi ko alama bai yarda da tsarin kayyade farashi ba kuma ba zai yi hakan ba, illa dai za su yi aiki tukuru su tabbatar sun samar da man a kasuwa.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023, lokacin jawabin karɓar mulki ne Bola Tinubu ya bayyana cire tallafin man fetur.
Masana da dama na kallon cire tallafin man fetur da barin kasuwa ta tantance darajar naira a matsayin abubuwan da suka ta’azzara matsalar tattalin arziƙi da al’ummar ƙasar suka faɗa ciki.
Tun bayan cire tallafin farashin man daga kusan naira 200 a kan lita daya zuwa sama da naira dubu daya abubuwa suka ta’azzara ga ‘yan kasar kasancewar man ya damfara ga yawancin harkokin rayuwar al’ummar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1464 days 15 hours 8 minutes 53 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1446 days 16 hours 50 minutes 18 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com