Home General Ku yi mana Addu’a domin samin Nasara

Ku yi mana Addu’a domin samin Nasara

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya su riƙa yi wa shugabanninsu addu’a, inda ya ce su ma suna buƙatar hakan tare da goyon baya domin ƙasar ta ci gaba.

Tinubu ya bayyana haka ne a saƙonsa na Kirsimeti, inda ya taya al’uumar Najeriya murna, tare da kira gare ga Kiristoci su yi amfani da ranar domin sabunta burinsu na samun ingantacciyar Najeriya.

Shugaban ya sake jajanta wa waɗanda suka rasu a turmutsutsun Oyo da Anambra da Abuja, inda ya ce shugabanni ma suna buƙatar addu’o’in domin su yi jagoranci nagari.

Ya kuma yi kira ga ƴan ƙasar su tuna marasa ƙarfi, musamman maƙwabta da ƴan’uwa da abokai da sauran abokan hulɗa.

“Shugabanni ma suna buƙatar addu’o’i da goyon baya. Idan muka samu goyon bayanku, za mu yi mulki nagari. Najeriya ta kama hanyar inganci domin alamu suna nuna cewa akwai haske a gaba.”

Ya kuma ce za su tabbatar dukkan masu tafiye-tafiye sun je inda za su je lafiya, ta hanyar tabbatar da tsaro da kuma samar da hanyoyin sufuri kyauta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp