Home General Ana fargabar harin jirgin soji kan lakurawa ya hallaka mutane da dama...

Ana fargabar harin jirgin soji kan lakurawa ya hallaka mutane da dama a Sokoto

Ana fargabar al’umma da dama sun mutu wasu kuma sun jikkata sakamakon wani hari da jirgin yaƙi na soji ya kai kan Lakurawa a wasu ƙauyuka da ke Sokoton Najeriya.

Harin jirgin saman da aka kai kan ƴan ta’addan Lakurawa ya sauka kan alummar wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Silame ta jihar Sokoto dake arewacin Najeriya

Kauyukan da harin ya shafa sun haɗa da Gidan Sama da Rumtuwa, kuma lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7 na safiyar yau Laraba.

Wani mazaunin yankin Silame mai suna Malam Yahya ya ce ƙauyukan na kusa da dajin Surame inda ake zargin maboyar Lakurawa ne da ƴan bindiga.

Wata majiya ta shaidawa Dailytrust cewa sama da mutum 10 ne suka mutu kuma da dama sun jikkata a sakamakon harin jirgin saman yaƙin.

Kawo yanzu babu wata sanarwa  daga hukumomin tsaro kan lamarin.

Shugaban ƙaramar hukumar Silame Alh. Abubakar Muhammad Daftarana ya tabbatar da harin inda ya ce suna bincike kan irin barnar da harin jirgin yaƙin ya yi a ƙauyukan.

Al’ummar ƙauyukan na zaune lami lafiya lokacin da jirgin yaƙin ya yi ruwan wuta kan jama’a

Ya yi wuri na tabbatar da adadin mutanen da harin ya kashe ko suka samu raunuka saboda har yanzu muna tattara bayanai

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp