Home General Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Kwamitin Kula Da Bada Tallafin Jini

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Kwamitin Kula Da Bada Tallafin Jini

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, ta kaddamar da Kwamitin kwararru wadanda zasu kula da ayyukan bada tallafin Jini a fadin jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusif ne ya jagoranci kaddamar da kwamitin, da nufin samar da tsarin da zai dinga tabbatar da inganci da kuma tsarin da ake bi wajen samar da jini ga marasa lafiyar da suke bukata.

A cewar sa, “Gwamnatin Kano ta dauki matakin ne a kokarin ta na kawo karshen matsalolin da ake fuskanta, wajen tabbatar da kyakkyawan yanayin samar da jini ga marasa lafiya da kuma kulawa da ajiyar sa, adan haka muna yabawa gwamnan Kano a bisa kulawar da yake bawa fannin lafiya a koda yaushe”.

Ya kuma bayyana kyakkyawan zaton da yake dashi na ganin cewar za’a samu nasarar da ake bukata, duba da ƙunshin mambobin kwamitin wanda ya ce an zaɓo su ne bisa cancanta da kwarewar su a fannin kiwon lafiya, harma ya hore su da suyi kokarin sauke nauyin da aka dora musu.

Da yake jawabi, Shugaban kwamitin, kuma Daraktan kula da ayyukan lafiya a hukumar kula da manyan Asibitocin jihar Kano, Dakta Musbahu Rabiu ya godewa Kwamishinan a bisa kyakkyawan zaton da yake musu, harma yasha alwashin cewa kwamitin zai yi aiki tukuru don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Aikin kwamitin shine hada hannu da masu ruwa da tsakin fannin lafiya domin samar da kayan aiki, ledar daukar jinin dama bawa ma’aikata bitar sanin makamar aiki domin inganta fannin.

Mambobin Kwamitin sun kunshi Daraktocin dakunan gwaje-gwaje, Malaman jinya, Daraktan mulki na hukumar kula da manyan Asibitocin jihar Kano, wakilan hukumar kula da Asibitoci masu zaman kansu, dana ma’aikatar lafiya a matakin farko, dama sauran dukkan wasu bangarorin dake da alaka da fannin lafiya a lungu da sako na jihar.

Sanarwar da Jami’in yada labaran Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi ya aiko wa jaridar PRNigeria ta ce, an nada kwararriyar nan a fannin bada tallafin Jini wato Dakta Hauwa Ibrahim a matsayin Sakatariyar kwamitin.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp