Ƙungiyar ƴan siyasar arewa ta League of Northern Democrats wato LND, wadda take ƙarƙashin shugabancin tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ta fara yunƙurin zama jam’iyyar siyasa domin fuskantar zaɓen shekarar 2027.
Ƙungiyar ta zargi jam’iyya mai mulki ta APC da babbar jam’iyyar adawa ta PDP da gazawa wajen ciyar da Naeriya gaba, sannan ta buƙaci ƙungiyoyin kudancin ƙasar da su shigo su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ceton ƙasar.
A wata sanarwa da guda cikin jagororin ƙungiyar, Dr Umar Arɗo, ya ce ƙungiyar ta LND za ta kawo sauyi tare da sake dawo da martabar ƙasar.
Ya ce rashin ingancin gwamnati ne ya jefa ƙasar cikin ƙangin talauci da rashin tsaro da rashin tabbas.
Sai dai tuni jam’iyyar APC ta mayar da martani, inda daraktan watsa labaranta, Alhaji Bala Ibrahim ya ce su dai ko gezau, domin a cewarsa, rikiɗewar ƙungiyar zuwa jam’iyyar siyasa ba barazana ba ce ga jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 6 hours 52 minutes 37 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 8 hours 34 minutes 2 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com