Home General Ƴan bindiga sun sake sace mutane 46 a jihar Zamfara ta Najeriya

Ƴan bindiga sun sake sace mutane 46 a jihar Zamfara ta Najeriya

Ƴan bindiga a jihar Zamfara ta Najeriya, sun yi garkuwa da aƙalla mutane 46 yayin wani hari da suka kai kan al’ummar garin Gana da ke jihar ta yankin arewa maso yammacin ƙasar, lamarin da ke zayyana bayyana yadda matsalolin tsaro ke ci gaba da ta’azzara a yankin duk da namijin ƙoƙarin da mahukuntan ƙasar ke iƙirarin yi don baiwa al’umma kariya.

Bayanan masu tayar da hankali na zuwa a dai dai lokacin da wasu majiyoyi ke cewa ɗan bindigar daji Dogo Giɗe ya sanyawa wasu garuruwa 23 a ƙaramar hukumar tsafe duk cikin jihar ta Zamfara harajin naira miliyan 100 bisa sharaɗin kai musu hari matuƙar suka gaza haɗa adadin kuɗin da ya nema, ko da ya ke a zantawar da sashen Hausa na RFI ya yi da mazauna yankin sun ce babu batu mai kama da wannan barazana.

Kafofin yaɗa labarai na ciki da wajen Najeriya sun ruwaito yadda gomman ƴan bindigar suka farmaki garin Gana a jihar Zamfara cikin ranakun ƙarshen mako tare da buɗe wuta kan jama’a wanda ya kai ga ƙone tarin gidajen da wuraren sana’ar jama’a gabanin sace tarin mutane ciki har da mata da ƙananan yara.

Wannan hari na zuwa bayan makamancinsa a watan da ya gabata, wanda shi ma ya kai ga sace tarin mutane, a wani yanayi da ake ganin dawowar makamantan hare-haren da kuwa garkuwa da mutane.

A lokuta da dama jami’an tsaron Najeriya na ci gaba da nanata cewa sun kame tarin jiga-jigan masu garkuwa da mutane a wannan jiha, yayinda suke neman wasu ruwa a jallo.

Kusan dukkanin jihohin yankin na arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar matsalolin ɓatagarin kama daga ƴan bindiga da kuma ƴan ta’addan waɗanda suka hana jama’a sakat tare da kassara harkokin noma da kasuwanci, lamarin da ya ta’azzara talauci da yunwar da al’umma ke fama da ita.

Ko a makon da ya gabata, sai da ƴan bindigar, suka tare wata motocin safa tare da banka mata wuta bayan sace ilahirin fasinjan da ke cikinta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp