Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abba Kabir Yusuf, ya ce aikin hidimta wa Kano ne a gabansa yanzu “ba neman wa’adin mulki na biyu ba”.
Gwamnan na mayar da martani ne game da kalaman da tsohon shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya yi a farkon makon nan game da shirinsu na ƙwace mulkin jihar daga jam’iyyar NNPP a zaɓen 2027.
Kakakin gwamnatin jihar ta Kano, Sanusi Dawakin Tofa, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa gwamnan ya yi martanin ne yayin taron tallafa wa mata a fadar gwamnatin jihar.
“Ba neman wa’adi na biyu ne ya fi damu na ba. Na fi damuwa da sauke nauyin alƙawurran da na ɗauka a wa’adin farko…kuma ina son mutanen Kano su yi min hukunci da ayyukana a ƙarshen mulkin,” a cewar gwamnan.
Jam’iyyar NNPP ta ƙwace mulkin Kano ne a zaɓen 2023 bayan APC ta yi wa’adin mulki biyu na shekara takwas ƙarƙashin Abdullahi Umar Ganduje.