Home General Kotu a Najeriya ta yi watsi da sabbin bukatun da Godwin Emefiele...

Kotu a Najeriya ta yi watsi da sabbin bukatun da Godwin Emefiele ya gabatar mata

Kotun hukunta manyan laifuka da ke jihar Legas a Najeriya, ta yi watsi da bukatar da tsohon gwamnan babban bankin kasara, Godwin Emefiele, ya shigar, yana kalubalantar hukuncin da wata kotu ta yanke bisa zargin badakalar dala biliyan 4.5 da kuma naira biliyan 2.8 da hukumar EFCC ta shigar a kansa.

Mai shari’a Rahman Oshodi, a hukuncin da ya yanke, ya ce kotu na da hurumin gurfanar da Emefiele da wanda ake tuhuma, Henry Omoile.

Sai dai alkalin kotun ya yi fatali da tuhume-tuhume hudu daga cikin tuhume-tuhume 26 da EFCC ta shigar a kan su.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Emefiele ne a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume 26, da suka shafi karkatar da kudaden da suka kai dala biliyan 4.5 ba bisa ka’ida ba da kuma Naira biliyan 2.8.

A ranar 12 ga Disamba, 2024, lauyan Emefiele, Mista Olalekan Ojo mai mukamin SAN, ya bayar da hujjar cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar a Legas.

Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dakatar da Emefiele a matsayin gwamnan CBN a ranar 14 ga Yuni, 2023.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp