Home General Tinubu zai tafi taron ɗorewar tattalin arziki a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

Tinubu zai tafi taron ɗorewar tattalin arziki a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai tafi ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar taron ɗorewar tattalin arziki na duniya ta 2025 (ADSW 2025).

Shugaban ƙasar, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci shugaba Tinubu domin halartar taron – wanda zai gudana tsakanin 12 zuwa 18 ga watan Janairu.

Taron – wanda zai samu halartar manyan shugabannin duniya, da masana da ƙungiyoyin fararen hula da ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki – zai tattauna nasarorin da aka samu a fannin tattalin arziki da zamantakewa, tare da lalubo hanyoyin ɗorewar ci gaban da aka samu.

Cikin sanarwar bulaguron da fadar shugaban Najeriya ta fitar, ta ce a taron Shugaba Tinubu zai jaddada manufofin gwamnatinsa, ciki har ci gaban tattalin arziki da makamashi da sufuri da fannin lafiya.

Haka kuma tawagar Najeriya a taron za ta gana da fadar sarkin ƙasar domin tattauna batutuwan da suka shafi ƙasashen biyu.

Ministan harkokin wajen ƙasar, Ambassador Yusuf Tuggar na daga cikin manyan jami’an gwamnatin da za su yi wa shugaban rakiya a taron, a cewar sanarwar.

Ana sa ran shugaban zai koma Najeriya bayan kammala taron ranar 16 ga watan Janairu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Kotu ta Tabbatar da Pantami a Matsayin Ɗan PDP, ta Umurci Sabon Zaɓen Fidda Gwani a GombeDaga Hannun Masu Garkuwa Zuwa Tsira: Shugaban Bungudu ya Kubuta, Sojoji Sun Kwato ShanuTsohon Shugaban Tsaron Google ya yi Gargaɗi Kan AI Zai Iya Cutar wa Mafi Girma ga Yara Fiye da Kafafen Sadarwa Na ZamaniNIMC ta Karyata Da'awar Bayyana Bayanan NINMutane 4 da ake Zargi da Hakar Ma'adanai ba Bisa Ka'ida ba Sun Mutu Sakamakon Ruftawar Rami a FilatoBa na jin Haushin Waɗanda Suka Watsar da ni - El-RufaiSojoji Sun Kama Masu Haƙar Ma'adinai ba Bisa Ka'ida ba Sun Kwato Kayan Aiki a Jihar NasarawaZaɓen 2027: IGP Disu ya Umarci Manyan Jami'ai da su Ƙarfafa Leken Asiri, da Shirye-shiryen Aiki2027: Ƙungiyar TMG ta Bukaci Atiku, Obi, Makinde, Sowore Su Tattauna Kan Ɗan Takara Ɗaya na Hadin KaiGwamnan Enugu Ya Naɗa Mataimaka 1012027: Ƙungiyar OK ta yi Watsi da Haɗakar NDC, ta Sha Alwashin Rike TsarintaMinistan Tsaro ya Jaddada Kudurin Najeriya na Wanzar da Zaman Lafiya a Duniya a Taron UNGA Karo Na 81Hukumar EFCC Ta Sake Bayyana Neman Tsohon Shugaban Fansho Maina Ruwa-a-JalloTinubu Zai Bai wa Mazauna Abuja Manyan Ayyuka Kyautar a Watan Disamba – WikeHukumar Kwastam ta Tantance Kusan Mutane 3,000 Yayin da Aikin Daukar Ma'aikata na 2025 ya Kare
X whatsapp