CBN ya ci tarar bankuna saboda rashin saka kuɗi a ATM

Babban bankin Najeriya CB ya ci tarar wasu bankunan kasuwanci na Najeriya saboda samun kuɗi a na’urorin cire kuɗi na ATM ɗinsu a lokacin bukuwan ƙarshen shekara.

Babban bankin ya tarar naira miliyan 150 ne kan kowane banki da ya samu da laifin, kuma bankunan sun haɗa da Fidelity da First Bank Plc da Keystone da Union da Globus da Providus da Zenith Bank da UBA da Sterling tarar naira miliyan 150.

A wata sanarwa da aka miƙa wa bankunan, an ce za a zare kuɗaɗen ne kai tsare daga asusun ajiyan bankunan da ke babban bankin,” kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

“CBN ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen cin tarar duk wani bankin da ya karya dokar tabbatar da yalwatar kuɗaɗe,” kamar yadda mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na bankin, Hakama Sidi Ali ya tabbatar.

Ya kuma ƙara da cewa za su cigaba da bibiyar masu ɓoye tsabar kuɗaɗe a bankuna da masu POS.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1463 days 6 hours 36 minutes 46 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1445 days 8 hours 18 minutes 11 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com