Home General Ana fargabar mutuwar tarin Sojin Najeriya a wani sabon harin ISWAP

Ana fargabar mutuwar tarin Sojin Najeriya a wani sabon harin ISWAP

Wasu rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce ƴan ta’adda sun sake farmakar ayarin Sojin ƙasar da ke kan hanyarsu ta laluben gawarwakin manoma 40 da ISWAP ta hallaka a garin Dumba na yankin Baga da ke ƙaramar hukumar Kukawa a jihar.

Wasu majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa mayaƙan ISWAP ne suka ƙaddamar da harin kuma har kawo yanzu babu cikakkun alƙaluman sojojin da aka rasa a wannan farmaki.

Wata majiya daga ɓangaren ƴan sa kan ta bayyana cewa tun da farko adadi mai yawa na Sojin Najeriya tare da ƴan sakai 54 ciki har da mafarauta ne suka shiga dajin don laluben gawarwakin sai dai har zuwa yanzu ɗan sa kai 1 ne tal ya dawo cikin Baga a galabaice.

A cewar bayanai sun ce da farko sojojin sun so daƙile harin ƴan ta’addan amma kuma yawan makaman da mayaƙan ke ɗauke da shi ya tilasta musu ja da baya.

Rahotanni sun ce babu tabbacin Soji nawa suka mutu ko kuma nawa suka jikkata haka zalika a ɓangaren mayaƙan na sa kai lura da cewa hatta mutum guda da ya dawo cikin gari baya cikin hayyacinsa da zai iya bayar da labarin abin da ya faru.

Sai dai wata majiya daga ɓangaren Sojin Najeriya ta ce tuni wasu daga cikin dakarun na ta suka dawo sansaninsu da ke Baga.

A cewar majiyoyin Sojin sun birne 15 daga cikin manoman da ƴan ta’addam suka kashe sai sun haɗu da farmaki a lokacin da suka kai tsakiyar hanya a ƙoƙarinsu na isa Dumba, amma sun ci gaba da tafiya bana kawar da barazanar ƴan ta’addan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp