Home General An sace kayan wutar lantarki a birnin Abuja

An sace kayan wutar lantarki a birnin Abuja

Hukumar rarraba lantarki ta Najeriya (TCN) ta sanar da cewa wasu mutane sun ɓarnata tare da sace kayan wuta da ke samar da lantarki ga wasu sassa na Abuja, babban birnin ƙasar.

Sanarwar da hukumar ta fitar a jiya Juma’a ta ce “an lalata layin wutar lantarkinta na 132kV da wayoyin ƙarƙashin ƙasa waɗanda ke kai lantarki zuwa cikin ƙwaryar Abuja da unguwannin da ke kewaye, lamarin da ya kawo katsewar lantarki”.

Lamarin dai ya jefa unguwannin Abuja da dama cikin duhu, tare da haifar da wahalahalu ga al’umma.

Sanarwar, wadda ta samu sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ndidi Mbah, ta ce wayoyin su ne ke kai lantarki ga cibiyoyin rarraba lantarki na kamfanin AEDC domin samar da lantarki ga al’umma.

“Lamarin wanda ya faru a kusa da Millenium Park da ke Abuja, ya shafi fiye da kashi 60 cikin ɗari na lantarkin da ake samar wa birnin,” in ji sanarwar.

Bayanin ya tabbatar da cewa maɓarnatan sun sace wayoyin lantarki da sauran kayan wuta da dama.

Unguwannin da abin ya shafa sun haɗa da Maitama, da Wuse, da Jabi, da Life Camp, da Asokoro, da Utako da kuma Mabushi.

Hukumar ta TCN ta ce ta tura jami’anta domin yin gyara a inda aka sace kayan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp