Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ake yadawa cewa ta sayi kowacce akuya cikin awakin da zata rabawa matan karkarkara a wani bangare na yunkurin gwamnatin jihar na tallafa musu kan farashin naira dubu 350.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya aike da manema labarai a yau Alhamis a birnin Kano.
Waiya ya ce an siyi Akuyoyi guda dubu 7158 kan kudi naira miliyan 451, inda za a raba wa mutane dubu 2386, sai Raguna guda 1975 kan kudi naira miliyan 351 da dudu 750 da za raba su ga mutane 987.
Haka zalika an siyi Shanu guda 1400 kan kudi naira biliyan 1 da miliyan 120 wadanda za a raba wa mutane 700, sai kuma kudin ciyarwa da magani da sauran hidinhimu da aka ware na naira miliyan 427 da dubu 958.
Read Also:
Kwamishinan ya kara da cewa jimullar kudin da aka ware sune naira Biliyan 2 da naira miliyan 350 sabanin abinda ake yada wa kan cewar kowacce akuya an siye ta kan naira dubu 350.
‘’’wannan shi ne abunda aka ware ko aka yi da su wato naira miliyan dubu 2 da naira miliyan 350 sabanin abinda mutane suke ta yamadidi da shi’’ Waiya.
Sai dai waiya ya yi zargin cewa an yada labarin da gangan dan a bata gwamnati har ya shawarci manema labarai su dinga bincike kafin su yada wani abu don kaucewa yada fitina a tsakanin al’umma.
‘’Wannan ba daidai ba ne yakamata al’umma su dinga jin tsoron Allah kan abubuwan da suke yi kuma su fahimci cewa ya madidi da abinda yake na zance na karya ba daidai ba ne’’ Waiya’’.
A karshe Waiya ya ce duk wanda ya duba jawabin gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana dukkan adadin kudaden da aka yi daki-daki.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1463 days 19 hours 12 minutes 42 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1445 days 20 hours 54 minutes 7 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com