Home AFIRKA ECOWAS ta tabbatar da ficewar Nijar, Burkina Faso da kuma Mali a...

ECOWAS ta tabbatar da ficewar Nijar, Burkina Faso da kuma Mali a hukumance

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta tabbatar da ficewar kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar a hukumance

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da ECOWAS din ta fitar, tana mai cewa har yanzu kofa a bude take ga wadannan kasashe, a duk lokacin da suka sauya shawarar sake koma wa.

A cikin sanarwar, ECOWAS ta ce za a ci gaba da mutunta fasfon jama’ar wadannan kasashe uku da ke dauke da tambarin ECOWAS, hadi da katinsu na shaidar dan kasa.

Haka zalika kungiyar ta ce za a ci gaba da kallon wadannan kasashe tamkar mambobinta, har ma ta bayyana a cikin sanarwar cewa, harkokin kasuwanci tsakanin kasashe mambobin ECOWAS da kuma kasashen Nijar, Burkina Faso da kuma Mali zasu ci gaba da tafiya kamar yadda suke a baya.

Sanarwar ta kuma bukaci kasashen kungiyar, da su ci gaba da bawa jama’ar kasashen uku damar shiga kasashensu ba tare da takardar izinin shiga ba, da kuma zama, har sai baba ta gani.

Kungiyar ta ce an fitar da wannan sanarwa ne, domin kaucewa haifar da zaman tankiya ko kuma dardar tsakanin jama’ar wadannan kasashe uku, musamman ‘yan kasuwa, da kuma kwantar musu da hankula.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp