Home General NDLEA ta kama matsala masu shaye -shaye 18 a Kano

NDLEA ta kama matsala masu shaye -shaye 18 a Kano

Hukumar hana sha da Fataucin miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kasa reshen jihar Kano, ta sami nasarar kama wasu Matasa 18 wadanda ta ke zargin suna da alaka da kayan maye.

Kakakin hukumar na jihar Sadik Muhammad Maigatari ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba manema labarai a ranar Jumu’a, inda ya ce nasarar ta samu ne ka karkashin “Operation Hana Maye”, wanda suke kokarin kakkabe dukkan wasu harkokin kayan maye ko kuma ta’ammali dasu a lungu da sako na jihar Kano.

A cewar hukumar, “Mun sami nasarar ne a wuraren da Matasan ke taruwa a unguwannin Fagge, Kwarin Kaya, Kofar Wambai, da kuma Kofar Mata, harma muka sami nasarar kama Tabar Wiwi, Sholisho da kuma makamai hadin gida masu haɗarin gaske”.

Haka kuma sanarwar ta kara da cewa, a yayin sumamen wasu gungun Matasa ɗauke da makamai sun fito suna yi wa jami’an hukumar barazana, amma sun sami nasarar kama biyu daga cikin su inda suke tsaka da neman ragowar domin su fuskanci hukunci.

A karshe hukumar ta bada tabbacin ci-gaba da fatattakar dukkan masu yin wata mu’amala da kayan maye a fadin jihar, ta yadda rayuwar al’umma zata inganta yadda ya kamata.

Gwagwarmayar Nemawa ‘Yan Najeriya Sauki Zakuyi Ba Iya Ma’aikata Ba – Sakon Gama Ga NLC

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp